A cikin shirin Dadin Kowa Kashi na 99 Ladidi ta kai karshen kulewa da halin Aminu AK, shine me ya biyo baya?....Rashin hadin kai a tsakanin iyalan M. malami yasa suna neman rasa gidan gadonsu....A yayin da da Dantani yake fafutukar neman Furera ta amince ta aure shi, an kama shi. Shin me Aminu AK ya yi lokacin da ya ji labarin cewa M. Kabiru zai yi aure?