Ayi dai mu gani! Timo ya faso Gari, har da sayen hannun jari. Shin mecece makomar Alawiyya bayan rusa zancen aurensu da Nuhu? A yayin da Malam Hassan ya matsa lamba don shiga hurumin da ba nasa ba, a can gefe kuma anya Zayyad baya shirin kulla wata kitimirmirar? Haduwar Haidar da Gimbiya a wannan karon, bamu san ko me Haidar din zai zo da shi ba. Dangwari da bakonsa Jawo, ko yaya zata kwashe musu? Don ganin yadda zata kaya, ku biyo mu a Shirin Dadin Kowa Kashi na 89.