Horon da Hansatu take yi wa Badaru ya sanya yayi Zuciyar da ta sanya shi yanke shawarar Neman gwaggwabar sana'ar da za ta iya rike shi ya tsayu da Kafarsa, yayin da shi Kuma Olabode ya fara nuna wa Stella irin kunar da ke ransa na kasancewar tana da wani Dan gaba da fatiha ba tare da ya taba sani ba a tsawon shekarun auren su. 'Yan'uwan Anaconda sun baza komar neman sa Lungu da Sako sakamakon batar da ya yi tun bayan harin da a ka kai garin Dadin kowa.